Yadda Ake Hadin Daidaita Al'ada Idan Tana Yawo Da Hankali

 

Yadda Ake Hadin Da Yake Daidaita Al'ada In Yana Yawo Da Hankali Zaki nemi kayan Hadi kamar haka;

* Man habbatus sauda

* Man albabunaj

* Man fijil

* Zuma

* Bayani;

Karanta>>> Maganin Kurajen Gaba Da Kaikayin Gaba Na Mata

Zaki samu wadannan mai din sai ki hadasu guri daya ki juya har hade sai ki dunga zubawa a cikin zuma kina sha safe da yamma, in sha Allahu zai daina damunki.

Wabillahi Taufiq.

Karanta>>> Amfanin Hulba A Jikin Yan Mata Dama Matan Aure.

Me ke janyo rikicewar jinin al'ada?

 

Matan da ba su wuce jinin haila ba kan fuskanci ciwo a kasan mararsu, kafin jinin al'adar ya fara zuba ko kuma bayan haka.

Hukumar Lafiya ta Burtaniya (NHS) ta ce ciwon mara abu ne da ya zama ruwan dare kuma wani ɓangare ne na haila. Kuma ciwon yakan dauki kwana biyu zuwa uku ko fiye ana yi.

Karanta>>> Amfanin Hulba Guda 21 Ga Lafiyar Jiki Musamman Yan Mata Da Matan Aure.

Sannan yakan zama matsananci ga wasu mata, yayin da wasu kuma yakan zo musu ne sama-sama, in ji hukumar.

Haka kuma wani sa'in wasu kan ji kwankwasonsu na ciwo, ko da ba lokacin jinin haila ba ne.

Mata na jin ciwon mara ne a cewar NHS idan naman da ke jikin mahaifa ya murɗe.

Karanta>>> Maganin Toilet Infection Da Izinin Allah

Kodayake, hakan na faruwa a kodayaushe, amma ba kasafai ake ji ba saboda a hankali yake yi.

Sai dai a lokacin jinin al'ada ya fi matsewa sosai domin ya taimaka wajen fitar da jinin.

Hukumar ta kara da cewa lokacin da mahaifar ke matsewa tana matse jijiyoyin jinin da ke jikinta, kuma a dalilin hakan sai jini da iskar Oxygen da ke kaiwa ga mahaifar ya katse.

To rashin iskar oxygen a mahaifar yana sa ta fitar da wasu sinadarai wadanda ke kara ciwon mara.

Karanta>>> Tusar Gaba Da Abinda Ke Kawota Yana Da Kyau Ku Karanta Wannan Bayanin

A yayin hakan ne kuma mahaifar ke fitar da wasu sinadaran na daban da su kuma suke sake kara murde ta sosai, kuma ciwon ya kara tsananta.

Baya ga wannan hanya, akwai wasu dalilai da kan janyo ciwon mara ga mace.

Ciwon marar da shan wasu magunguna ko wasu abubuwa na asibiti ke haifarwa ya fi shafar matan da suka fara girma. Lamarin ya fi shafar mata masu shekara 30 zuwa 45 sosai.

Karanta>>> Yadda Zaki Haɗa Ingantaccen Maganin Ciwon Sanyi (Infection)

Amma a cewar NHS, idan ciwon marar da suke yi ba shi da wani dalilin da ke janyo shi, mata na samun sauki idan suna kara girma.

Kazalika, mata da dama ne ke samun saukin ciwon marar idan sun fara haihuwa.

Sannan a mafi yawan lokaci, akan ji sauki idan an dauki wasu matakai a gida waɗanda ba sai an je asibiti ba.

Karanta>>> Sirrin Mallakar Miji Ba Boka Ba Malam

Amma idan yanayin ciwon marar ya yi tsanani sosai ko mace ta ga wani sauyi a zubar jini ko wani abin da ba ta saba gani ba, to hukumar tana bayar da shawarar a je a ga likita.

Post a Comment

0 Comments

Ads